1 Corinthians 7

1Game da abubuwan da kuka rubuto: “Yayi kyau ga mutum kada ya taba mace.” 2Amma Saboda jarabobi na ayyukan fasikanci masu yawa, ya kamata kowane mutum ya kasance da matarsa, kowace mace kuma ta kasance da mijinta.

3Kowanne maigidanci ya ba matarsa hakin ta, kuma kowace mace ta ba maigidan ta hakinsa na saduwa da juna. 4Matan ba ta da iko akan jikin ta amma maigidan ne. Haka ma, maigidan bashi da iko akan jikinsa amma matar ce.

5Kada ku hana wa junanku saduwa, sai dai da yardar junanku domin wani dan lokaci. Kuyi haka domin ku bada kanku ga addu’a. Daganan sai ku sake saduwa, domin kada Shaidan ya jarabce ku saboda rashin kamun kanku. 6Amma ina fada maku wadannan abubuwa ne a matsayin nuni, ba a matsayin umurni ba. 7Na so da kowa da kowa kamar ni yake. Amma kowa na da baiwarsa daga wurin Allah. Wani na da irin wannan baiwar, wani kuma waccan.

8Ga marasa aure da gwamraye, Ina cewa, yana da kyau a garesu su zauna ba aure, kamar yadda nike. 9Amma idan baza su iya kame kansu ba, ya kamata su yi aure. Gama yafi masu kyau su yi aure da su kuna da sha’awa.

10Ga masu aure kwa, ina bada wannan umarni- ba ni ba, amma Ubangiji: “Kada mace ta rabu da mijinta.” 11Amma idan har ta rabu da mijinta, sai ta zauna ba aure ko kuma ta shirya da shi. Haka kuma “Kada miji ya saki matarsa.”

12Amma ga sauran ina cewa-Ni, ba Ubangiji ba-idan wani dan’uwa yana da mata wadda ba mai bi ba, kuma idan ta yarda ta zauna da shi, to kada ya sake ta. 13Idan kuwa mace tana da miji marar bi, idan ya yarda ya zauna tare da ita, to kada ta kashe aure da shi. 14Gama miji marar bada gaskiya ya zama kebabbe saboda matarsa, sannan mata marar bada gaskiya ta zama kebbiya saboda mijinta mai bi. In ba haka ba ‘ya’yanku za su zama marasa tsarki, amma a zahiri su kebabbu ne.

15Amma idan abokin aure marar bi ya fita, a bar shi ya tafi. A irin wannan hali, dan’uwa ko ‘yar’uwa ba a daure suke ga alkawarinsu ba. Allah ya kira mu da mu zauna cikin salama. 16Yaya kika sani, ke mace, ko za ki ceci mijinki? ko yaya ka sani, kai miji, ko za ka ceci matarka?

17Bari dai kowa ya yi rayuwar da Ubangiji ya aiyana masa, kamar yadda Allah ya kirawo shi. Wannan ce ka’idata a dukkan ikilisiyu. 18Mutum na da kaciya sa’adda aka kira shi ga bada gaskiya? Kada yayi kokarin bayyana kamar marar kaciya. Mutum ba shi da kaciya sa’adda aka kira ga bangaskiya? To kada ya bidi kaciya. 19Gama kaciya ko rashin kaciya ba shine mahimmin abu ba. Mahimmin abu shine biyayya da dokokin Allah.

20Kowa ya tsaya cikin kiran da yake lokacin da Allah ya kira shi ga bada gaskiya. 21Kai bawa ne lokacin da Allah ya kirawo ka? Kada ka damu da haka. Amma idan kana da zarafin samun ‘yanci, ka yi haka. 22Domin wanda Ubangiji ya kira shi lokacin da yake bawa, shi ‘yantacce ne na Ubangiji. Hakanan kuma, wanda shike ‘yantacce lokacin da aka kira shi ga bada gaskiya, Bawan Almasihu ne. 23An saye ku da tsada, donhaka kada ku zama bayin mutane. 24Yan’uwa, a kowace irin rayuwa kowannenmu ke ciki lokacin da aka kira mu ga bada gaskiya, bari mu tsaya a haka.

25Game da wadanda basu taba aure ba, ba ni da wani umarni daga wurin Ubangiji. Amma ina bada ra’ayina kamar mutum wanda, ta wurin jinkan Allah, yake yardajje. 26Don haka, Ina ganin saboda yamutsin dake tafe ba da jimawa ba, ya yi kyau mutum ya zauna yadda yake.

27Kana daure da mace? Kada ka nemi ‘yanci daga gare ta. Baka daure da mace? Kada ka nemi auren mace. 28Amma idan ka yi aure, ba ka yi zunubi ba. Kuma idan mace marar aure ta yi aure, bata yi zunubi ba. Saidai su wadanda suka yi aure za sha wahalhalu iri-iri a yayinda suke raye, kuma ina so in raba ku da su.

29Amma wannan nike fadi ya’nuwa: lokaci ya kure. Daga yanzu, bari wadanda suke da mata suyi rayuwa kamar basu da su. 30Masu kuka su zama kamar marasa kuka, masu farinciki kamar marasa farinciki, masu sayen abubuwa kamar marasa komai. 31Wadanda suke harka da duniya kamar ba su harka da ita, domin ka’idar duniyan nan tana kawowa ga karshe.

32Ina so ku kubuta daga damuwa mai yawa. Mutum marar aure yana tunani akan al’amuran Ubangiji, yadda zai gamshe shi. 33Amma mai aure yana tunani akan al’amuran duniya, yadda za ya gamshi matarsa, 34hankalinsa ya rabu. Mace marar aure ko budurwa tana tunanin al’amuran Ubangiji, yadda za ta kebe kanta a jiki da ruhu. Amma mace mai aure tana tunanin al’amuran duniya, yadda za ta gamshi mijinta.

35Ina fadar wannan domin amfaninku ne, ba domin in takura ku ba. Na fadi wannan domin abinda ke daidai, yadda zaku bi Ubangiji ba tare da hankalinku ya rabu ba.

36Amma idan wani yana tunani da cewa baya yin abinda ya dace ga budurwarsa- idan ta wuce shekarun aure, kuma hakan ya zama dole- sai yayi abinda yake so. Ba zunubi yake yi ba. Sai suyi aure. 37Amma idan ya tsaya da karfi a zuciyarsa, idan baya shan wani matsi kuma yana iya kame kansa, har ya kudurta a zuciyarsa yayi haka, wato ya kiyaye budurwarsa da yake tashi, to hakan ya yi daidai. 38Don haka, shi wanda ya auri budurwarsa yayi daidai, sannan shi wanda ya zabi yaki yin aure yafi yin daidai.

39Mace tana a daure ga mijinta a duk tsawon rayuwarsa. Amma idan mijin ya mutu, tana da ‘yanci ta auri duk wanda take so ta aura, amma a cikin Ubangiji. Amma a ganina, za ta fi farinciki idan za ta zauna yadda take. Kuma ina tunanin ni ma ina da Ruhun Allah.

40

Copyright information for HauULB